Featured
Ƴan bindiga sun sace limamai 6 bayan halartar taron addu’ar neman nasarar Tinubu a 2027

Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da sace wasu malaman addinin Musulunci shida a jihar Zamfara. An ce lamarin ya faru ne ranar Asabar, bayan limaman sun halarci wani taron addu’a na neman nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.yayin da ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an sace su a gidan tsohon gwamnan jihar, Sanata Abdul’aziz Yari, da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara.
Rundunar ta bayyana cewa an sace malaman ne a kan hanyarsu ta tafiya daga yankin dajin Sububu da ke ƙaramar hukumar Bakura zuwa Talata Mafara.
Read Also : Nan gaba hannun jarin matatar mu zai iya tashi daga 525 zuwa 10,000 – Dangote
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar.
Sanarwar wadda aka fitar ranar Lahadi, ta kawo karshen rahotannin da ake yadawa na cewa lamarin ya faru a gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari.