Featured
Rikicin Boko Haram ya lalata makarantu sama da 5,000 a Borno – Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce rikicin Boko Haram ya lalata gine-ginen makarantu sama da 5,000, tare da sabbaba barin yara kimanin miliyan 2.2 ba sa zuwa makaranta, musamman a lokacin da rikicin ya yi kamari.
Zulum ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Maiduguri, yayin da Gwamnan Nasarawa, Abdullahi A. Sule, ya ƙaddamar da wasu ayyuka.
Daga cikin ayyukan akwai gadar Post Office, da makarantu, da kuma hanyar da aka faɗaɗa daga Budum Tandari Junction zuwa Kasuwan Shanu.
Gwamnan ya ce baya ga lalacewar gine-ginen makarantu, malamai da masu kula da makarantu da dama sun rasa rayukansu, yayin gudanar da ayyukansu.