Connect with us

Featured

Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci Ta Jihar Kano Ya Yi Murabus 

Shugaban Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Saidu Yahaya, ya yi murabus daga muƙaminsa. Daily Trust ta rawaito cewa Yahaya ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne ranar Talata, bayan matsin lamba da ake zargin ya fuskanta daga gwamnatin jihar.

Ko da yake ba a sanar da murabus ɗin a hukumance ba, gwamnatin jihar ta nuna cewa an riga an naɗa sabon shugabanci a hukumar. Mai ba Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan kafafen sada zumunta, Ibrahim Adam, ya sanar da cewa an naɗa Barrister Hafsat Ada’u Kutama a matsayin mukaddashiyar shugabar hukumar.

Read Also : Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin Kano da muzgunawa ƴan adawa

Kutama, wadda a baya take riƙe da muƙamin Sakatariyar hukumar, za ta fara aiki a matsayin shugaba mai riƙon ƙwarya daga ranar Laraba. Tun da farko an naɗa Saidu Yahaya a matsayin shugaban hukumar a watan Agustan 2025, bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, kuma Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da naɗin na tsawon shekaru biyar.

Murabus ɗin Yahaya ya zo ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi suka kan yadda hukumar ke gudanar da aikinta, inda ya bukaci shugaban hukumar ya ƙara kaimi wajen yaƙi da cin hanci.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Wasu ƴan Najeriya sun roƙeni na rage wutar lantarkin da muke samarwa saboda firinjinsu ya fara daskarewa - Ministan Lantarki - KAKAKI 24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet