Featured
Ban taɓa ganin shugaban ƙasa mai kyawawan tsare-tsare kamar Tinubu ba — Masari
Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce tsare-tsaren Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga Nijeriya sun fi na duk wani shugaban ƙasa da ya taɓa gani a kusan shekaru 40 da ya shafe yana siyasa.
Masari ya bayyana hakan ne a wani taron jama’a a Kaduna, inda ya ce ra’ayinsa ya samo asali ne daga dogon lokaci da ya shafe yana cikin harkokin siyasar Nijeriya. Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar da su mara wa gwamnatin baya fiye da sukar da ake yi wa gwamnatin Tinubu.
Read Also : Zaɓen 2027 tsakanin APC da ƴan Najeriya za a yi shi – Makinde
Tsohon kakakin Majalisar Wakilai ya ce irin sukar da ake yi wa gwamnatin Tinubu ta taɓa biyo bayan gwamnatocin Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan. Ya ce abinda aka yi wa wadancan gwamnatocin, su ne ake amfani da su wajen sukar gwamnatin yanzu.
Masari ya kuma yi kira ga mata masu wa’azi da su yi amfani da tasirinsu wajen hana kalaman da za su iya ƙara rarrabuwar kawuna ta fuskar addini da ƙabila, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da irin waɗannan batutuwa domin biyan buƙatun siyasa ba.
