Featured
Ina rokon ƴan Najeriya su bani dama na kammala ayyukan alherin da na fara – Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa na gyara kura-kurai da kuma damar da gwamnatocin baya suka rasa, domin kawo ci gaba a kasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, yayin addu’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Kasa da ke Abuja domin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Read Also : PDP ta sanya ranar gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a Gombe
Ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su yanke kauna ba, domin a yanzu zaman lafiya da ci gaba na dawowa kasar, kuma abubuwa za su inganta yadda ya kamata, duba da yadda dimokuradiyya ke ci gaba da samun gindin zama.
Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su kara bai wa gwamnatinsa dama domin ta kammala ayyukan da ta fara, yana mai cewa Najeriya na kan hanyar da ta dace kuma akwai haske a karshen tafiyar.
