Featured
Ƴan bindiga sun hallaka sojoji 8 da fararen hula 4 a Zamfara

Wani hari da ’yan bindiga suka kai a jihar Zamfara ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 13, ciki har da sojoji, yayin da suke rakiyar wasu ’yan kasuwa a hanyar Gwashi, da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum.
Bayanai sun ce ’yan bindigar sun yi wa ayarin motocin kwanton ɓauna ne, inda suka buɗe musu wuta. Honarabul Hamisu A. Faro, ɗan majalisar dokoki mai wakiltar Bukkuyum ta Kudu, ya ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji takwas da fararen hula huɗu.
Read Also : Sabon Harin Houthi Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum Ɗaya a Filin Jirgin Sama na Riyadh
Ya ƙara da cewa wani jami’in tsaro guda ɗaya ya rasu a asibiti, yayin da kauyuka fiye da biyar ke cikin firgici. Manoma kuma sun gaza zuwa gonakinsu domin girbe amfanin da suka noma saboda tsoron sace su ko kashe su, lamarin da ya raba kusan mutum 5,000 da muhallansu.
Al’ummar yankin ta bakin ɗan majalisar, ta buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki kai tsaye kan wuraren da ’yan bindigar ke buya. Ya ce ƙin yin sulhu da ’yan bindigar da gwamnati ta yi a baya-bayan nan ya ƙara tsananta lamarin, inda suka ɗauki alwashin tarwatsa al’ummomin yankin Bukkuyum.