Featured
Tinubu ba zai je Zamfara, Katsina da Neja domin gudanar da yaƙin neman zaɓe ba

Shugabannin jam’iyyar APC ne za su wakilci Shugaba Bola Tinubu a jihohi sama da 20 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen 2027, wanda za a fara a Jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoba, 2026, kamar yadda jadawalin kamfen ɗin jam’iyyar ya nuna.
Jadawalin ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu zai halarci gangamin a jihohi 12. Waɗannan sun haɗa da Kaduna ranar 24 ga Oktoba, Port Harcourt a Rivers ranar 7 ga Nuwamba, Jos a Plateau ranar 14 ga Nuwamba, Ibadan a Oyo ranar 21 ga Nuwamba, Maiduguri a Borno ranar 25 ga Nuwamba, Enugu ranar 28 ga Nuwamba da Bauchi ranar 29 ga Nuwamba.
Read Also : Gov Buni Inaugurates 2 Commissioners, LG Chairmen; Charges Officials On Service Delivery, Party Loyalty
A watan Disamba, an tsara Tinubu zai halarci gangamin Sokoto ranar 4 ga Disamba, Asaba a Jihar Delta ranar 12 ga Disamba da Kano ranar 17 ga Disamba. Za a ci gaba da gangamin a sabuwar shekara, inda aka tsara Yola a Jihar Adamawa ranar 4 ga Janairu, 2027.
A ƙarshe, an ware Jihar Legas domin gudanar da babban gangamin rufe kamfen ɗin ranar 9 ga Janairu, 2027. Wannan shi ne jadawalin da aka gabatar na gangamin APC da Tinubu zai halarta, yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar babban zaɓen 2027.
Read Also : Gwamnatin Zamfara Za Ta Siya Wa Mutane 36,176 Hannayen Jari a Kamfanin Dangote
Jihohin da Tinubu zai halarta — 12
1.Kaduna — 24 Oktoba 2026
2. Rivers — 7 Nuwamba 2026
3. Plateau — 14 Nuwamba 2026
4. Oyo — 21 Nuwamba 2026
5. Borno — 25 Nuwamba 2026
6. Enugu — 28 Nuwamba 2026
7. Bauchi — 29 Nuwamba 2026
8. Sokoto — 5 Disamba 2026
9. Delta — 12 Disamba 2026
10. Kano — 17 Disamba 2026
11. Adamawa — 4 Janairu 2027
12. Lagos — 9 Janairu 2027
Sauron jihohi 24 da birnin tarayya Abuja shugabannin APC ne za su wakilce shi.
Tinubu ya bayyana a baya cewa ba zai halarci dukkan gangamin APC ba saboda yana son daidaita harkokin kamfen da gudanar da gwamnati.
Pingback: Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci - KAKAKI 24