Featured
NCC Ta Ƙaddamar Da Manhajar Tantance Wayoyi a Najeriya

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ƙaddamar da wata sabuwar manhajar tantance wayoyi mai suna Device Checker Platform, domin tabbatar da bin ƙa’idojin fasaha da kuma yaƙi da yaɗuwar wayoyin bogi, waɗanda aka kwaikwaya ko aka shigo da su ba tare da izini ba a ƙasar.
Mai kula da ofishin hukumar na shiyyar Kano, Injiniya Maigana Gidado, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai kan matakan hukumar na tabbatar da ingancin fasaha da tsaron hanyoyin sadarwa, wanda aka gudanar a ofishin NCC da ke Kano ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026.
Gidado ya ce ƙaddamar da manhajar ya zama wajibi sakamakon bunƙasar tattalin arzikin zamani na Najeriya, domin tabbatar da cewa na’urorin da ke amfani da katin SIM wajen haɗuwa da hanyoyin sadarwa suna bin ƙa’idojin fasaha da dokokin da aka shimfiɗa.
Ya bayyana cewa hukumar ta sauƙaƙa hanyoyin samun lasisi da kuma daidaita matsayin masu sana’ar sayar da na’urorin sadarwa a Jihar Kano. Haka kuma, ta gudanar da wayar da kai ga masu shigo da kaya da sauran masu ruwa da tsaki a Legas da wasu sassan ƙasar, domin ƙara fahimtar ƙa’idojin amincewa da na’urori kafin amfani da su.
Read Also : Tinubu zai gabatar da kasafin 2027 kafin ƙarshen shekara
A cewarsa, manhajar za ta bai wa masu ruwa da tsaki damar tantance lambar IMEI ta kowace na’ura da kuma ɗora bayananta kai tsaye a tsarin. Ya kuma shawarci masu sayen waya da su tabbatar da sahihancinta kafin saye ta hanyar ziyartar shafin **http://www.ncc.gov.ng/devicechecker**, yayin da masu sana’ar na’urori za su iya amfani da **https://imeiscanner.registermydevice.ng/**. Haka kuma, akwai jagorar tantance na’urori a **http://www.ncc.gov.ng/DeviceCheckerGuide**.
Mai kula da ofishin ya jaddada cewa manhajar ba ta da alaƙa da sa ido kan mutane, kuma ba ta shiga saƙonninsu, hotunansu, lambobin wayoyinsu ko bayanan kuɗinsu. Ya buƙaci jama’a su riƙa tantance wayoyi kafin saye, su saya daga hannun dillalai masu lasisi, sannan su yi amfani da layin kyauta na hukumar mai lamba 315 domin neman bayani ko taimako.
A nata ɓangaren, Babbar Manajar Fasaha da Tsaron Hanyoyin Sadarwa, Miss Kingi Bayi, ta bayyana cewa sabuwar dokar ta shafi shigo da kayan sadarwa ne, ba na’urorin da jama’a ke amfani da su a halin yanzu ba. Ta ce hukumar za ta tabbatar da bin ƙa’idojin izinin shigo da na’urori da amfani da manhajar, inda za a fara nuna na’urorin da ba a yi wa rajista ba domin a yi musu rajista kafin ɗaukar matakin toshe su. Ta ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen gano wayoyin jabu da waɗanda aka kwaikwaya, tare da ƙarfafa kariya daga satar waya, zamba da fallasa bayanan sirrin jama’a.
Pingback: Kano : Kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da shaye-shaye da fadan daba ya kama 'Malam Keya' bisa zargin jagorantar kungiyoyin ƴan daba a Dala - KAKAKI 24