Connect with us

Featured

Da ɗumi ɗumi : Ƴar Kwankwaso ta buƙaci Kotu ta raba auren su da Abba Gida-gida

Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ta shigar da ƙarar neman raba aurensu a wata kotu da ke Gudu, Abuja, bisa tsarin Khul’i da Musulunci ya tanada.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa takardun kotu sun nuna cewa Zainab, ’yar tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta nemi a raba auren ne saboda rashin kulawa, soyayya da kusanci tsakanin ma’auratan. Ta kuma bayyana cewa a yanzu ba ta sha’awar ci gaba da zaman auren.

A cikin ƙarar, Zainab ta ce ƙoƙarin sasanta tsakaninsu ya ci tura, tana mai bayyana fargabar cewa ci gaba da auren zai iya hana ta sauke wasu wajibai na addinin Musulunci. Ta kuma nuna aniyarta ta mayar da sadakin da aka biya mata domin samun damar raba auren. Kotun ta umarci gwamnan da ya gurfana a gabanta ranar 17 ga Nuwamba, 2026.

Rahoton ya ƙara da cewa ma’auratan sun yi aure ne a ranar 29 ga Yuli, 2006, kuma suna da ’ya’ya shida. Haka kuma, an ce Zainab ta bar gidan gwamnatin Kano zuwa gidan mahaifinta kafin daga bisani ta tafi Abuja, lamarin da ya jawo binciken wasu jami’an tsaro. Sai dai Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano, Sanusi Dawakin Tofa, bai mayar da martani kan batun ba.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet