Featured
Atiku ya yi alkawarin magance matsalar tsaro, farfado da tattalin arziki idan aka zaɓe shi

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin magance matsalar tsaro da farfado da tattalin arzikin Najeriya idan aka zaɓe shi a babban zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC da aka gudanar a filin wasa na Dabo Aliyu da ke Potiskum, cibiyar kasuwancin jihar Yobe.
Ya kuma yi alƙawarin samar da damarmaki ga matasa domin su cimma burinsu da kuma gudanar da ayyukan da suka zaɓa a rayuwarsu, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani nau’in tashin hankali ba.
“Duk abin da kuke son yi, gwamnatina za ta tallafa muku, amma ba za mu bari a riƙa aikata abubuwan tashin hankali ba,” in ji Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar samar da man fetur da wutar lantarki a farashi mai sauƙi, tare da rage haraji domin sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya matsin tattalin arziki.
Ya buƙaci ‘yan Najeriya da su mara wa ADC baya a zaɓen 2027, yana mai cewa cika waɗannan alƙawura ya danganta da yadda masu zaɓe za su fito domin zaɓen jam’iyyar.
Atiku ya kuma yi kira ga masu zaɓe da su yi amfani da hankalinsu wajen zaɓar shugabanni nagari, tare da guje wa siyasar son kai da rashin gaskiya.
“Ku zaɓi jam’iyyar ADC domin makomarku da makomar yaranku, domin muna shirye mu bauta muku ta kowace hanya da za mu iya,” in ji shi.
Tun da farko, Sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya gode wa al’ummar jihar Yobe bisa kyakkyawar tarbar da suka yi wa tawagar jam’iyyar.
Aregbesola ya buƙaci masu zaɓe da su goyi bayan yunƙurin jam’iyyar na kawo sauyi a harkokin siyasa, tare da tabbatar da gaskiya da adalci wajen ƙirga da tattara ƙuri’u a zaɓen 2027.
A nasa ɓangaren, wasu magoya bayan jam’iyyar ADC da suka halarci gangamin sun bayyana kwarin gwiwarsu kan damar jam’iyyar na samun nasara a zaɓen mai zuwa, inda suka yi alƙawarin zaɓen ‘yan takararta a dukkan matakan siyasa.
Sun bayyana cewa goyon bayansu ga jam’iyyar ya samo asali ne daga buƙatar samun sauyi, musamman ganin halin matsin tattalin arziki da suke dangantawa da cire tallafin man fetur da manufofin haraji na gwamnatin yanzu.
Sun ce suna fatan sauyin gwamnati zai kawo sauƙi ga ‘yan Najeriya ta hanyar inganta tattalin arziki da samar da manufofin da za su rage wa magidanta nauyin rayuwa.
“Muna shirye mu zaɓi jam’iyyar ADC daga sama har ƙasa, domin ‘yan Najeriya suna buƙatar sauyi. Wahalar rayuwa ta yi yawa, kuma muna ganin sabuwar gwamnati za ta iya kawo sauƙin da ake buƙata,” in ji wani magoyin bayan jam’iyyar.
Shi ma Malam Umar Usman, ɗaya daga cikin magoya bayan ADC, ya bayyana cewa tashin farashin kayayyaki da nauyin haraji sun ƙara tsananta halin da talakawa ke ciki.
Ya ce, “Muna son gwamnatin da za ta saurari jama’a kuma ta magance matsalolin tattalin arzikinsu.”
A cewarsa, cire tallafin man fetur da kuma wasu manufofin haraji na gwamnatin yanzu sun ƙara tsananta wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
“Saboda haka, muna da cikakken yaƙinin cewa jam’iyyar ADC za ta iya samar da madadin da ya fi kyau,” in ji shi.
Gangamin ya samu halartar dubban magoya bayan jam’iyyar, ciki har da matasa, mata da tsofaffi, waɗanda suka fito domin tarbar Atiku Abubakar da tawagarsa.
Pingback: Najeriya na asarar maƙuden kuɗaɗe saboda haramta tabar wiwi - Sowore - KAKAKI 24