Featured
Kwankwaso Ya Musanta Aika Gwamna Abba Wajen Tinubu Domin Tattaunawa Kan Komawa APC
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta zargin cewa shi ne ya aika Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wajen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin tattaunawa kan shirin komawarsu jam’iyyar APC.
Sanata Kwankwaso ya musanta zargin ne cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Dakta Habibu Mohammed, ya fitar a ranar Litinin.
Read Also : Zaɓen 2027: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar ɗan takarar gwamnan Kano a NDC zuwa Disamba
Sanarwar ta bayyana cewa zargin da Gwamna Abba ya yi a hirarsa da BBC Hausa wani yunƙuri ne na ɗora wa Kwankwaso alhakin matakan siyasarsa. Ta kuma jaddada cewa tattaunawar siyasa ba ta nufin an samu yarjejeniyar da za ta ɗaure dukkan ƙungiyar Kwankwasiyya.
Haka kuma, ƙungiyar ta ƙalubalanci Gwamna Abba da ya gabatar da sahihan hujjoji kan yarjejeniyar da yake ikirarin an cimma, ciki har da lokacin da aka yi ta, waɗanda suka halarta da kuma sharuɗɗanta. Ta kuma ce sam Kwankwaso ba shi da alhakin matakin da gwamnan ya ɗauka na komawa APC a watan Janairun 2026.
