Tsaro
Jigawa: Ƴan sanda sun cafke mutumin da ke kai wa ƴan bindiga dabbobi

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, ta ce ta cafke wani matashi mai shekaru 25 da ta ke zargi yana kai wa ƴan bindiga dabbobi cikin dazuka.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP Lawan Shisu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar.
Sanarwar ta ce, rundunar ta cafke shi ne da shanu 73 da kuma raguna 13.
Haka kuma ta cikin sanarwar ya ƙara da cewa za su gurfanar da shi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike a kansa.