Connect with us

Labarai

Neja: Ƴan bindiga sun sace fasinjoji 13

Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta tabbatar da sace wasu fasinjoji 13 da wasu ƴan bindiga suka yi a kauyen Konar Barau da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Mista Monday Kuryas, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai da yammacin yau Laraba a Minna babban birnin jihar.

Mista Monday Kuryas ya ce, da misalin ƙarfe 3:30 na ranar Larabar nan ne baturen ƴan sanda na Zungeru ya sanar da shalƙwatar jihar faruwar lamarin.

Ya ce, wani mutun ne mai suna Mubarak Idris mazaunin ƙauyen Kwanawa ta jihar Sokoto wanda kuma direban motar bas mai lamba LGT 12 XWX dauke da fasinjoji 18 daga Yawuri jihar Kebbi galibi masunta ne da za su je birnin Yenagoa da ke jihar Beyelsa shi ne ya kai musu rahoton sace fasinjojin.

Ya ce, direban ya shaida musu cewa, lokacin da suka iso kwanar Barau da ke yankin ƙaramar hukumar Rafi a kan hanyar Tegina zuwa Minna ne ɓata garin cikin kayan sojoji suka sace fasinjojinsa 13 da yaron motarsa.

Haka kuma direban ya ce, ƴan bindigar sun kuma kwace masa kuɗi har Naira 131,500.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet