Labarai
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kashe magajin Al-barnawiy Malam Baƙo

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da rahoton mutuwar magajin jagoran ƙungiyar ƴan tada ƙayar baya ISWAP Malam Bako wanda ya karɓi ragama ƙungiyar bayan hallaka Al-barnawiy.
Mai bai wa shugaban Buhari shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Mongonu mai ritaya ne ya tabbatar da mutuwar tasa a ganawarsa da manema labaran fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
Mongonu ya bayyana bayan hakan ne bayan da ya kammala ganawa kan harkokin tsaro a fadar ta Villa jiya Alhamis.
Ya ce, Malam Bako ya mutu ne lokacin da yake tare da jiga-jigan ƙungiyar ta ISWAP.