Labarai
Sarkin Ningi ya yi barazanar tuɓe masu alaƙa da ƴan bindiga

Mai martaba sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya sha alwashin tuɓe duk mai rawani da ke da alaƙa da ƴan bindiga.
Sarkin ya yi wannan gargaɗi ne yayin wani taron gaggawa da ya yi da masu rike da sarautu na masarautarsa.
Ya ce, “Ba mu da tarihin wani mai sarautar gargajiya da ya taba hada kai da ‘yan bindiga da masarautar Ningi, sai dai na kadu da jin yadda aka ce an samu wasu mutane a karamar hukumar NIngi masu alaka da bata garin.’’
Mai martaba Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya kara da cewa, “Mun kaddamar da wani Kwamitin bincike domin gano mana duk wanda ke da alaka da bata garin, kuma zamu tube duk wanda aka samu da wannan laifi.
Haka kuma ya ce, gwamnatin jihar ba za ta lamunci rashin da a rashin kishin jihar ba daga kowanne mai rike da sarautar gargajiya ba, kuma muna da goyon bayan gwamnatin kan wannan batu don tabbatar da zaman lafiya da cigaban al’umma.
Dailytrust ta ruwaito cewa, ko a taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar ranar Litinin din da ta gabata, gwamnan jihar ta Bauchi Bala Mohammed ya yi zargin cewa, akwai masu rike da sarautar gargajiya da suke da alaka da ‘yan bindiga.