Labarai
Kogi: Yan sanda sun cafe masu garkuwa da mutane 3

Rundunar yan sandan jihar Kogi, ta ce ta cafke wasu mutane uku da ta ke zargin su da yin garkuwa da mutane tare da aikata sauran wasu manyan laifuka a hanyar Itobe zuwa Ajaokuta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP William Ayah, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin jiya Asabar.
Sanarwar ta ce, yan sandan sun yi nasarar kwato makamai da alburusai da na’urar cirar kudi ta POS da wasu layu masu yawa duk a hannun bata garin.
Ta cikinnn Sanarwar DSP William Ayah, ya kara da cewa, “Sakamakon ayyukan masu aikata muggan laifuka da suka addabi yankin Itobe da kewayenta musamman babbar hanyar Itobe zuwa Anyigba, a ranar 16 ga wannan wata na Oktoba jami’an yan sanda da ke aiki a ofishin Itobe karkashin Rundunar Yankin Ajaokuta, sun kama mutanen.
Sanarwa ta ce Waɗan aka cafke sun haɗar da: Danlami Shauibu da Kabiru Amodu, duka mazauna ƙauyen Adumu ne waɗanda ake zargi da alhakin jerin ayyukan garkuwa da mutane a yankin.
Haka kuma ya ce, “Rundunar yan sandan ta cafke wadanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike na sirri domin dakile ayyukan masu aikata laifuka a yankin.’’
Sanarwar ta kara da cewa, Wadanda ake zargin sun amsa cewa suna cikin gungun bata garin da ke da hannu ayyukan ta’addanci a babbar hanyar Itobe zuwa Anyigba.
Mai magana da yawubn rindinar yan sandan ta jihar Kogi, ya kara da cewa, “Yayin binciken farko, guda cikin wadanda suka cafke din, ya bai wa rundunar muhimman bayanai wanda ta hakan hukumar ta cafke wani wanda ake zargi mai suna Adejoh Tijani a ranar 22ga wannan wata da misalin karfe 8:30 na safe.