Tsaro
Shugabannin majalisun dokokin jihohi sun buƙaci Shugaba Buhari ya ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda

Kungiyar shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana ayyukan yan bindiga da yin garkuwa da mutane a matsayin ayyukan ta’addanci.
Shugabannin sun bukaci hakan ne a taron wanni tara na shekarar nan da muke ciki wanda suka gudanar a fadar gwamnatin jihar Katsina jiya Asabar.
Haka kuma yan majalisar, sun yi tir da Alla-wadai bisa tabarbarewar harkokin tsaron Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar a karshen makonnan.
Shugaban kungiyar kuma shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Suleiman, ne ya karanta sanarwar ga manema labarai.
Ya ce, “Taron ya sake yin Allah wadai da yawaitar rashin tsaro a kasar nan tare da yanke shawarar aiwatar da tsarin dokoki don taimakawa kokarin gwamnatin tarayya na yaki da rashin tsaro a a Najeriya baki daya.
Ya kara da cewa, “Taron ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana ta’addanci da ayyukan masu garkuwa da mutane a matsayin ta’addanci, ta haka ne za a yi maganin masu aikata munanan laifukan cikin gaggawa.