Tsaro
Ƴan bindiga sun sace malamai 4 na jami’ar Abuja tare da iyalansu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari Jami’ar birnin tarayyar.
Wasu mazauna Jami’ar da suka nemi a sakaye suna su, sun shaida wa manema labarai cewa, ƴan bindigar sun kutsa kai gidajen ma’aikatan jami’ar Jami’ar da ke Gwagwalada da misalin karfe 1:00 na daren wayewar yau Talata.
Rahotanni sun ce, ƴan bindigar sun ci ƙarfin masu gadin Jami’ar ne ta hakan suka samu kutsawa har sashen ma’aikatan.
Sai dai da safiyar yau ne shugaban sashen yaɗa labaran jami’ar Dakta Habib Yakoob, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafin Facebook na jami’ar.
Haka kuma ya ƙara da cewa ana nan ana ƙoƙarin ganin cewa an ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya.