Labarai
Katsina: Ƴan sanda sun cafke Malamin da ya sace ɗan yayansa

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce, ta cafke wani malamin makarantar Islamiyya bisa zargin sa da sace ɗan uwansa don neman kuɗin fansa.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isah, ya fitar.
Sanarwar ta ruwaito cewa, ƴan sanda sun kama malamin ne mai suna Jamilu Idris wanda ke yankin ƙaramar hukumar Faskari bisa zargin sace dan ɗan uwan nasa mai suna Umar Farouk Kabir, ɗan shekara 4 da haihuwa.
Haka kuma ta cikin sanarwar, rundunar ƴan sandan ta ce, ranar 9 ga watan jiya na Oktoba ne Jamilu ya je gidan mahaifin yaron Kabiru Abdullahi wanda ke zaune a Funtua, ya sace yaron inda ya kai shi Dutsen-Alhaji da ke birnin tarayya Abuja.
Haka kuma rundunar ta ƙara da cewa daga nan ne Jamilu ya kira yayan nasa ya buƙaci kuɗin fansa har naira miliyan 5.
Haka kuma sanarwar ta rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce, Jamilu ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, don haka za su gurfanar da shi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.