Labarai
Yadda Ƴan bindiga suka buɗe wuta kan masu karɓar ta’aziyya

Rahotonni daga jihar Benue na nuni da cewa, wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 4 a wani hari da suka kai wajen wani zama makoki a ƙauyen unguwar Mbayatyo Mbater da ke yankin ƙaramar hukumar Logo.
Jaridar The Nation, ta ruwaito cewa, mazauna ƙauyen sun ce, mahara sun lkai farmaki ne a daren wayewar yau Lahadi inda suka buɗe wuta akan mutane.
Baya ga waɗnda suka rasun kuma wasu sun samu raunika inda aka garzaya da su asibiti.
A nasa ɓngaren, Shugaban ƙaramar hukumar ta Logo Mista Aber Isaac, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labari.