Connect with us

Labarai

An gudanar da taron farfaɗo da martabar Arewacin Najeriya a Kano

Kungiyar farfado da martabar Arewa (NRO) ta gudanar da wani taro na musamman inda ta tattaro masu ruwa da tsaki da dattawan yankin Arewa domin tattauna kalubalen yankin Arewa a jihar Kano.

Taron wanda ya gudana a jiya Lahadi yana daga cikin ƙoƙarin da su ke yi na magance matsalolin da ke ƙara ta’azzara a yankin da yanzu haka ke ƙaruwa cikin wani yanayi mai ban tsoro, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yana daga cikin aikin kungiyar na maido da jituwa da dauwamammen zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da maido da halayya da kuma asalin mutuncin Arewa.

Da yake jawabi, Shugaban kungiyar ta NRO, Malam Gidado Mukhtar, ya koka da yadda shugabanci ke rasa ingancinsa, manufa da kuma tasirinsa, ya kara da cewa akwai bukatar a kawo gyara cikin gaggawa.

A nasa ɓangaren Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce kasancewar yankin Arewa yana da harsuna kusan 320, ba za a iya haɗe shi ba sai dai idan mutum ya san menene yankin duk da bambancin addini da kuma sauran bambance-bambance.

Shi ma da yake nasa jawabin, Alhaji Bashir Othman Tofa, ya jaddada bukatar Arewa ta tashi tsaye domin yin magana da murya daya, inda ya bayyana kasala, hassada, kiyayya, rashin aikin yi da rashin aiwatar da manufofi a matsayin muhimman batutuwan da ke haifar da barazana.

A cewarsa: “Mun zabi shugabanni su yi mana aiki amma sun koma bautar da mu. Muna da dubban abubuwan da ba mu san yadda za mu magance su ba.

“Ba mu da hadin kai, ba ma kaunar junanmu. Me zai faru idan babu Najeriya?”

Wani dattijon Arewa, Musa Magami, ya yi kira ga kowa da kowa da su hada kai, yana mai cewa an mayar da masana’antun Arewa zuwa mafi kaskanci saboda rashin kulawa da aka yi shekaru da yawa. Ya kara da cewa Saudiyya ta taba shiga cikin wannan hali kuma a yau ta hanyar daukar matakan da suka dace suna daya daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya.

Kungiyar ta NRO tana da mambobi sama da 600 da ke da tushe a Kano kuma tana da alaka da wasu kungiyoyi 15 wadanda na agaji ne.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet