Uncategorized
Yadda ƴan sanda su ka cafke Aljan ƙasurgumin ɓarawon babur mai ƙafa uku a Kano

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da cafke ƙasurgumin ɓarawon babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da adaidaita-sahu a Kano, ko kuma nafe a sauran jihohi.
Shi dai wannan ɓarawo mai suna Sabitu Ibrahim, wanda aka fi sani da Aljan, ɗan kimanin shekaru 18, daga garin Kaburma Ƴan Daddawa, cikin karamar hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano ya ke.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a jiya Asabar da daddare, gungun ƴan sanda na sashin Kan-ka-ce-kwabo, wanda rundunar ta ke kira da Operation Puff Ada, ƙarƙashin jagorancin SP Buba Yusuf ne su ka samu nasarar kama Aljan.
Kiyawa ya ce an kama shi ne da wani babu mai ƙafa uku, wanda ya ke dauke da lamba GRR77QA da kuma lambar KAROTA KMC 1106.
Kakakin ya baiyana cewa sunan Aljan na cikin jerin sunayen ma su laifi da rundunar ke nema ruwa a jallo.
Kiyawa, mai muƙamin DSP, ya ƙara baiyana cewa a yayin binciken ƙwaƙwaf, Aljan ya amsa cewa tabbas ya hada baki da wani su ka tare wani matuƙin babur mai ƙafa uku a Ɗorayi.
Ya ƙara da cewa Aljan ya bada bayanin cewa bayan sun tare matuƙin babur mai ƙafa ukun, sai su ka yi amfani da waya su ka shaƙe wuyanshi da niyyar su hallaka shi, amma Allah Ya taimake shi ya kufce ya gudu da raunuka a jikinsa.
Bayan nan ne, in ji Kiyawa, sai Alhaj da abokinsa su ka tsere da wannan babur ɗin, inda ya ƙara da cewa da shine babur ɗin da a ka kama shi da shi.
Da a ka faɗaɗa bincike na sirri, inji Kiyawa, sai a ka kamo wani Abdullahi Sulaiman mai shekaru 28, ɗan unguwar Gwale da kuma Abubakar Muhammed mai shekaru 21 ɗan unguwar Hausawa duk a birnin Kano, bisa zarginsu da siyan wasu sassa na babur ɗin da Aljan ya k5wace, da kuma wani babur mai lamba FGE212QX, sai kuma lambar KAROTA 4636 KMC, da aka same su a tare dasu.
Kiyawa ya bada lambar waya 08105359575 ga wadanda aka sace musu waɗannan babura da su tuntuɓi rundunar, ko kuma su tuntubi kakakin kai tsaye.
Kwamishinan Yan Sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya godewa al’ummar jihar Kano baki daya bisa gudummawa ta addu’a, kwarin gwiwa da kuma goyon baya da suke basu, ya bukaci a cigaba da basu hadin kai wajen gudanar da ayyukansu, musamman addu’a da kuma kai rahoto ga ofishin yan sanda mafi kusa idan aka lura da wani abu da ba’a yarda dashi ba.