Connect with us

Labarai

Hukumar KSCPC A Kano Ta Kori Ma’aikata kusan 100

Akalla ma’aikatan agaji 100 na Hukumar Kare hakkin masu saye da siyarwa ta jihar Kano CPC sun rasa aikinsu sakamakon sauya wanda zai shugabanci hukumar.

KakakiHausa ta rawaito cewa, Idan za a iya tunawa a watan Afrilu ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da ‘yan sa kai 100 wadan da galibinsu masu digiri ne a matsayin ma’aikatan da zasu tallafa a majalisar, wanda za a rika byansu albashin Naira 10,000 a kowane wata.

Kwatsam kuma, sabon Shugaban Majalisar, Janar Idris Bello Dambazau (mai ritaya), ya karbi ragamar mulki daga hannun Bappa Baba Dan’Agundi, Manajan Darakta na Hukumar Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) cikin watan Afrilu da korar masu aikin sa kai.

Sakamakon haka, masu aikin sa kai 100 sun roki gwamnan jihar da ya binciki ayyukan majalisar dangane da karya dokokin da suka kafa majalisar.

Takardar koken mai dauke da sa hannun Hayat A Yusuf da kuma Usman Rabiu Muhammad, shugaba da sakatare, sun bayyana cewa sabon hafsan ya dakatar da biyan su alawus na wata-wata cikin watanni uku da suka gabata.

Masu aikin sa-kai sun ce, “muna cikin nasarorin da majalisar ta samu, an gano ma’ajiyar miyagun kwayoyi, kuma ayyukan barayin muggan kwayoyi sun tsaya da taimakon mu.”

A martanin da jami’in yada labarai na majalisar Malam Musbahu Hassan ya mayar kan ikirari na ‘yan sa kai, ya ce ba a kori kowa ba.

Musbahu ya ce, “Ba mu kori kowa ba sai wadan da suka daina zuwa ofishin, kuma kamar yadda nake magana da ku, muna da sama da 50 daga cikin ‘yan sa kai a tare da mu, kuma mun kara musu alawus daga N10,000 zuwa N30,000.

Rikici dai ya barke yayin da hukumar Kano ta kori ma’aikata sama da 100.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet