Connect with us

Labarai

Bauchi: Mutane 16 Sun Rasa Rayukansu A Wani Hatsarin Mota – FRCN

Yusuf Abdullahi, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, yace akalla mutane 16 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku a jihar ranar Lahadi.

Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira daya yi da manema labarai ranar Litinin a Bauchi.

A cewarsa, hatsarin ya rutsa da wata babbar mota da kuma wata motar kirar Toyota Hummer ta kasuwanci, a kauyen Bambal dake kan titin Kano zuwa Jama’are da karfe 7:00 na dare.

Kwamandan sashin, wanda yace sai da jami’an sa suka dauki kimanin mintuna bakwai kafin su isa wurin domin baiwa wadanda lamarin ya rutsa dasu agajin gaggawa, tare da share wurin da lamarin ya faru, sannan ya danganta hatsarin da gudu daya wuce kima.

Ya kara da cewa“Mutane 16 ne hatsarin ya rutsa dasu da suka hada da maza 10 da mata shida kuma dukkan mutanen dake cikin motar sun rasa rayukansu a hadarin.

“ Motar Bas din Hummer ta Kama da wuta bayan ta bugi motar kuma babu wani rai daya tsira daga cikin hatsarin.

Kazalika “ wasu mutanen sun kone ta yadda ba a iya gane su a cikin motar Tiyota Hummer,” in ji Abdullahi.

Sannan ya bayyana cewa an ajiye gawarwakin mutanen da abin ya shafa a dakin ajiye gawa na babban asibitin Kiyawa dake hanyar Kano zuwa Jama’are domin tantancewa.

Kwamandan sashin ya shawarci masu ababen hawa dasu kasance masu bin ka’idojin tuki da na zirga-zirgar ababen hawa a kodayaushe yayin da suke bin hanyoyin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet