Featured
Yanzu Yanzu: Ganduje Ya Dawo Daga Kwas Ɗin Koyon Dabarun Mulki

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nmandi Azikiwe da ke babban birnin tarayya Abuja, bayan shafe tsawon mako guda a wata makaranta mai suna Harvard Business School, a birnin Boston na America, da yaje don samun horo akan dabarun mulki.
A makon jiya ne kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, kwamared Muhammad Garba, ya bayyana cewa gwamna Ganduje ya miƙa ragamar shugabancin jihar a hannun mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, kuma dukkan masu muƙaman gwamnati za su yi aiki da mataimakin ne idan buƙatar hakan ta taso.