Connect with us

Labarai

Kaduna: Ƴan bindiga Sun Kashe Aƙalla Mutane 9 A Wasu Ƙananan Hukumomi

Akalla mutane tara ne aka kashe a wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a wasu kananan hukumomi hudu na jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar harin da adadin wadan da suka mutu.

Ya lissafa yankunan da abin ya shafa sun hada da Chikun, Igabi, Zaria, da Zango Kataf.

A cewar Aruwan, mutane uku ne suka mutu yayin da wani mutum kuma ya samu raunuka sanda wasu ‘yan bindiga suka kai hari Buruku-Udawa da ke hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a karamar hukumar Chikun.

Ya kara da cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum daya a yankin Yola-Kadi, da kuma a karamar hukumar Chikun, yayin da wani mazaunin garin ya samu rauni a harin.

Haka zalika, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu a kauyen Sako da ke karamar hukumar Zangon Kataf, inda jami’an tsaro suka gano gawarwaki biyu a yankin Kurfi-Magamiya a karamar hukumar.

A Zariya, mutum daya ya rasa ransa bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Saye da ke cikin karamar hukumar, wanda ya kawo adadin wadanda aka kashe zuwa tara.

A nasa jawabin, Gwamna Nasir El-Rufai yayi Allah wadai da hare-haren tare da addu’ar Allah ya jikan wadan da ‘yan bindiga suka kashe.

Ya kuma yi wa wadan da suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa tare da yin kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen yaki da masu aikata laifuka a fadin jihar.

Labarin na baya-bayan nan ya samo asali ne mako guda bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Rilwanu Gadagau.

Gadagau, wanda ya wakilci mazabar Giwa kuma ya rike mukamin shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi da raya karkara, an kashe shi ne a daren ranar Litinin.

Yana daga cikin matafiya da dama da barayin suka yi garkuwa da su, wadan da suka yi kwanton bauna a babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya. Majiyarmu ta bayyana cewa an dauki sama da sa’o’i biyu ana gudanar da harin a babbar hanyar.

Kwanaki biyu bayan faruwar lamarin, an gano gawar dan majalisar a kusa da Mawai, wani kauye mai tazarar kilomita 13 daga babban birnin jihar Kaduna.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet