Connect with us

Labarai

Atiku ne ya fi cancanta da takarar shugabancin Najeriya a PDP – Salihu Tanko Yakasai

Tsohon mai baiwa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, shawara kan harkokin yaɗa labarai, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa Atiku Abubakar ne ya fi cancanta da dacewa ya yi takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023.

Tanko Yakasai ya bayyana hakan a yau a cikin wani dogon rubutu da ya yi a shafinsa na facebook da ke da nasaba da takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyun APC da PDP.

Ga dai labarin da Salihu Tanko Yakasai ɗin ya yi kamar haka:

“Wato na kan yi mamakin siyasa irin ta wasu, musamman a wajen zabin ra’ayin mutum a kan maganar yin takara ko a jiha, ko a matakin tarayya!

Naga ra’ayi ya bambanta sosai musamman a Arewa akan maganar tsayawa takarar shugabancin kasar nan da Jagaban Siyasar Nigeria wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wadda ya tabbatar da zai yi.

Na farko dai, jam’iyu su ne motar da kowa zai hau idan za shi tashar kujerar mulki, ko ta tsayawa zabe, ko ta mukami na nadi. Ke nan a Nigeria a yanzu, jam’iyyu biyu ne masu karfin da za su iya sa wa a zabi shugabanni a ƙasar nan, ko jam’iyyar APC, ko kuma jam’iyyar PDP.

Abinda su ka tsayar shi sauran ƴan ƙasa za su zaba. A yanzu yadda ake, a jam’iyyar APC mutum biyu ne alamu suka nuna za su iya samun damar a tsaida su takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da kuma Farfesa Yemi Osinbajo. Ita kuwa jam’iyar PDP, ba hurumina bane na ce ga wanda za su tsayar, maganar su ce ta siyasar cikin gida saboda ni shekara ashirin da biyu ina siyasa ban taɓa yin PDP ba, sai dai idan san samu ne, toh Wazirin Adamawa wato Alhaji Atiku Abubakar shi ya fi cancanta ya zamar masu dan takara. Wannan matsalar su ce!

A matsayin ka na dan APC, idan dai siyasar kake dole ka zabi daya daga cikin biyun can ka goyi bayan su, wanda ni a waje na duk tafiyar su daya a karshe hade kai za suyi, kuma duk wanda ya samu ticket ni zan yi shi, sai dai na yi laakari da wasu dalilai wanda nan gaba zan zaiyana su, wadanda suka sa na karbi goron gaiyatar Asiwaju a yanzu, kuma ni bana siyasa dan abin duniya, da ina yi da ban bi Buhari ba tsahon shekaru ashirin. Kuma idan dai abin duniya ne, inaga kowanne bangare zai iya bawa masu yi dan wannan, dan haka wannan ba hujja ba ce da zata sa na yi dan takara.

Ta wani bangaren kuma, idan ka ce duk baka san wadannan yan takarar, sai aka ce ma ga wata tafiyar, musamman ta matasa, shin matasa nawa ne zasu bi bayan wannan tafiyar? Idan har da wani tsari sabo, ingantacce wanda zai zamar mana masalaha ta samun chanji a kasar nan, toh a nuna min shi domin mu bi. Amma dai kawo yanzu, ba’a samar da wanman tsari ba.

Ni ina siyasa ta ra’ayi, da kishi! Bata neman abin duniya ba. Wannan tarbiyar ce mahaifina da sauran manyan yan siyasar mu mazan jiya suka koya min. Shekara ashirin ina yin Buhari, mahaifina kuma baya yin sa kowa ya sani, amma bai hana ni yi ba, kuma dama ba shi ya sani ba. Sannan a yanzu kowa ra’ayin sa yabi, duk da a wannan karan ra’ayin na mu ya zo daya. Wannan itace siyasa ta akida, ta yanci, kuma ni akan ta nake.

Ni ba wanda zan tursasa wa ya bi wani ɗan takara a zaɓen 2023, wallahi duk wanda ka ga ya da ce ka zaɓa ka zaɓa, na san cewa ukun nan da na lissafa ma, In sha Allah duk wanda ya samu a cikin su za a samu ci gaba a ƙasar nan. Babu wanda zan yi faɗa da shi ko nai maka baƙar magana akan zaɓen 2023, kowa yai wa kan sa hisabi. Idan har aka samu wata tafiya da na ga tafi wannan da na dauka, toh ni mai ajiye wannan ne na ɗau sabuwar.

Daga ƙarshe, ni abinda na rika a 2023 shi ne Allah!!! Na bar masa zabi, duk wanda yafi alheri a kasar nan Allah zaba mana shi, Ya kuma tabbatar mana da shi. Ba wai wanda na ke so ba, dan naga inda wanda nake so ya kai mu! A matsayi na na dan siyasa kuma, dole na zabi layi. Daga karshe addu’ar mu ita ce, Allah shige mana gaba a ƙasar nan amin!”
”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet