Connect with us

Kasuwanci

Har yanzu matuƙa Baburan Adaidaita Sahu ba su janye yajin aiki a Kano ba – Abba Hikima

Lauyan da ke kare gamayyar ƙungiyoyin matuƙa Baburan Adaidaita Sahu a jihar Kano, Abba Hikima, ya bayyana cewa har kawo yanzu mambobin kungiyar ba su janye yajin aikin da su ke yi ba.

Abba Hikim ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na facebook.

Sanarwar ta ce “A matsayina na lauyan gamayyar masu tuƙa bubaran Adaidaita sahu na jahar Kano, kuma ɗaya daga cikin wakilan su a sulhun da ake sa ran yi da gwamnatin jihar Kano, ta hanyar Kakakin Majalisar Dokokin Jahar Kano, ina mai sanar da jama’a cewa har yanzu daren Talata 11/1/2022, ba a samu wata matsaya da gwamnati ba sakamakon kafewa da gwamnatin tayi na akan matsayar ta“.

Haka kuma sanarwar ta yi kira ga al’ummar Kano da su yi watsi da labaran da wasu kafafen yaɗa labarai ke rawaito da ke bayyana cewa an janye yajin aikin.

“Saboda haka duk kokarin da wasu suke yi na yada farfaganda cewa an janye wannan yajin aiki to suna magana ne ba da yawun wadanda suka kira wannan yajin aiki ba”.

Hakazalika sanarwar ta jinjinawa matuƙa Baburan Adaidaita Sahun saboda juriyar da su ka nu na wajen bin doka da oda. “Ina so inyi amfani da wannan dama in jinjinawa matuka waɗannan babura domin juriya da suke nunawa cikin bin doka da sanin ya kamata“.

Yajin aikin mako guda da masu baburan A-Daidaita-Sahu a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya suka fara a ranar Litinin 9 ga watan nan na ci gaba da jefa al’ummar jihar cikin mawuyacin hali.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet