Connect with us

Labarai

Mawaƙan Kano: Tagwayen Asali sun auri ƴan uwansu tagwaye

Fitattun mawaƙan zamani, Hausa Hip-hop a Jihar Kano, Tagwayen Asali, sun auri ƴan uwansu tagwaye, Hassana da Hussaina, ƴan asalin Jihar Katsina.

Tagwayen Asali sun zaburar da magoya bayan su da masana’antar waƙoƙin zamani da auren zankaɗa-zankaɗan ƴan biyu masu kama ɗaya.

Haka kuma Tagwayen Asali sun daɗe su na jan hankalin magoya bayan su duba da irin shigar su iri ɗaya, su yi waka tare, sannan su na aiki a wata ma’aikata ta Gwamnatin Taraiya tare.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan biyun sun ce sun daɗe su na yin addu’a, har da ma azumi domin Allah Ya basu mata ƴan tagwaye da ga Katsina su aura.

“Mun dade muna addu’ar Allah Ya bamu mata ƴan biyu kuma sai gashi Allah Ya amsa addu’ar mu mun samu,” in ji su.

Ƴan tagwaye daban-daban ne su ka halarci ɗaurin aure da bikin na su domin su taya su murna da sa albarka.

Sannan kuma fitaccaen mawaƙin Hausa, Hamisu Breaker ne ya nishaɗantar da mahalarta a yayin bikin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet