Featured
Dan Takarar Shugabancin Najeriya Kuma Jigon Jam’iyyar APC Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Jihar Oyo

Jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma dan takarar shugaban kasa a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya ziyarci iyalan marigayi Christopher Alao-Akala a Ogbomosho.
Ziyarar dai ita ce ta’aziyya ga iyalansa bisa rasuwar tsohon gwamnan jihar Oyo.
Ya kuma kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Soun of Ogbomosho, Oba Jimoh Oyewunmi Ajagungbade III.