Featured
An yi wa Tinubu ihun “Ba ma yi” yayin Sallar Juma’ah a Abuja

Wasu matasa sun yi wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ihu jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a Masallacin Shehu Shagari da ke Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ayarin motocin shugaban ƙasar ke barin harabar masallacin, inda wasu suka rika rera taken “Ba mu yi, ba ma so” da kuma “Tinubu Must Go”.
Read Also : Ba ma goyon bayan wani ɗan takara a zaɓen 2027 – ASUU
Wasu shaidun gani da ido sun ce matakin da jami’an tsaro suka ɗauka na hana masu ibada shiga masallacin bayan isowar shugaban, tare da hana su fita har sai ya bar wurin, na daga cikin abubuwan da suka fusata jama’a.
A yayin sallar, Limamin masallacin, Rabiu Suleiman, ya gabatar da wa’azi kan darussan da ke cikin Suratul Fatiha, tare da addu’ar samun zaman lafiya da ƙarin lafiya da hikima ga Tinubu. Shugaban ya halarci sallar tare da Nuhu Ribadu, Femi Gbajabiamila da Abdullahi Ganduje, da sauran jami’ai.