Featured
Ba dan Tinubu ba, da tuni tattalin arzikin Najeriya ya durƙushe — Shettima

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce da ba don matakan da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka ba, da tattalin arzikin ƙasar ya durƙushe. Ya bayyana hakan ne a wani taro da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya a Fadar Shugaban Ƙasa, domin yaƙin neman sake zaɓen Tinubu a 2027.
Shettima ya amince cewa ’yan Najeriya sun sha wahalhalun tattalin arziki, amma ya ce lamarin zai fi haka muni idan ba don matakan gwamnatin Tinubu ba. Ya kuma soki masu sukar shugaban, yana mai cewa ya kamata a yaba masa maimakon a zarge shi.
Read Also : Zai fi min sauki a kulleni a gidan yari da a raba ni da wayata – Dangote
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaban kashi 4.43 cikin 100 a zangon baya-bayan nan, yayin da ajiyar kuɗaɗen ƙasar waje ta kai kusan dala biliyan 60. Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin za ta ɗauki sabbin matakai kan matsalolin noma, waɗanda yake fatan za su taimaka wajen rage farashin kayan abinci.
Shettima ya buƙaci matasa da su yaɗa saƙon manufofin gyaran tattalin arzikin gwamnatin ga sauran ’yan Najeriya. Ya ce matakan da Tinubu ya ɗauka na da muhimmanci wajen sake fasalin tattalin arzikin ƙasar, duk da ƙalubalen da al’umma ke fuskanta.
Pingback: Al’ummar Kano Atiku Za Su Zaɓa - KAKAKI 24