Connect with us

Labarai

Ƴan sanda sun kuɓutar da wani matashi da aka kusa yi wa yankan rago a Dambatta

Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kuɓutar da wani matashi da ake zargin wasu yan damfara sun yi yunƙurin yi wa yankan rago.

Lamarin ya faru ne a wani gida a ƙaramar hukumar Dambatta a Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan DSP Abdullahi Kiyawa ya shaida wa manema labarai cewa sun sami labarin faruwar lamarin ne bayan da matashin da aka fara yankawa makogoro ya kai musu ƙorafi.

Ya ce nan take suka garzaya da shi asibiti.

Matashin, mai shekara 23, ya bayyana wa BBC cewa a dandalin sada zumunta na Facebook suka haɗu da wanda ake zargi da yunƙurin halaka shi.

A makon da ya gabata ma an kama wani matashi da ya yi wa wata yarinya ‘yar makotansu yankan rago a karamar hukumar Tofa a Kano, bayan ya nemi kudin fansa daga wajen iyayenta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet