Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano na shirin gudanar da auren zawarawa

Kwamishiniyar kula da harkokin mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad ta baiyana cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa wajen gudanar da shirin nan ba da daɗewa ba.

Ta kuma bayyana cewa shirin zai gudana ne ta hanyar ma’aikatar kula da mata, inda ta ƙara da cewa kuma za ta zaɓi marayu da marasa galihu a sanya su a cikin shirin.

Dakta Zahra’u ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labaran Ma’aikatar, Bahijja Malam Kabara ta fitar a yau Lahadi.

Sanarwar ta ce Dr. Zahra’u ta yi bayanin hakan ne a lokacin wani taron daurin aure na mutane 31 maza da mata, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a yau Lahadi.

A cewar ta, matsalar tattalin arziki, sakamakon annobar korona na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da su ka sanya a ka samu tsaiko a shirin auren zawarawa da ƴan mata da Gwamnatin Kano ta saba yi.

Daga nan sai ta yi kira ga ma’aurata da su yi biyayya ga juna, kuma su bi ka’idojin aure kamar yadda ya ke a addinin Musulunci.

Kwamishiniyar ta kuma yaba da ƙoƙarin Gidauniyar FOMWAN da DARUL ARQAM da su ka shirya taron, ta re da yin kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan kyakkyawan misali.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet