Labarai
Kotu a Kano ta ci tarar hukumar KAROTA saboda cin zarafin wasu matasa

Wata babbar kotun jiha da ke unguwar Bompai a jihar Kano, karkashin jagorancin shari’a, jostis Nasiru Saminu, taci tarar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jiha (KAROTA) kudi kimanin Naira dubu dari shida, bisa laifin cin zarafin wasu matasa da kotun tace Karota tayi.
Hukumar Karota ta kama wasu matasa ne akan babur saboda sunyi goyo, harma taci tararsu, abinda kotun tace hakan cin zarafi ne, tunda dai ba babur din haya bane, don haka Karota bata da hurumin kamen goyo a babur.
Wadanda suka yi karar hukumar Karota su uku, Bello Basi Fagge, Lamin Ibrahim Adam da kuma Ibrahim Abdullahi, za’a biyasu Naira dubu dari biyar, kuma za’a biyasu kudin kara Naira dubu dari.