Labarai
Wata Kotu a Kano ta aike da Danbilki Kwamanda gidan yari

Wata kotu a jihar Kano ta aike da Abdulmalik Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan yari
Danbilki wanda shi ne shugaban ƙungiyar Arewa Media Group, zai gaba da zama a gidan yari har zuwa 15 ga watan Maris.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Danbilki Kwamanda ne daya daga cikin makusanta ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.
Ana tuhumarsa da batawa gwamnan Kano suna, kan zargin cewar gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka bai wa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.