Connect with us

Labarai

Idan Ajali Yayi Kira: Ƴar shekara 16 ta rasu a rijiya a Kano

Wata yarinya ƴar shekara 16, mai suna Hamida Bawale ta rasu bayan ta faɗa rijiya a yankin unguwar Kofar Fada Gidan Sarki da ke Ƙaramar Hukumar Karaye a Jihar Kano, jiya Talata.

Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiyan.

Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin jiya Talata, bayan da Hukumar ta karbi kiran gaggawa da ga ofishin Hukumar Kare Farar-hula, NSCDC, reshen Karaye da misalin ƙarfe 4:58.

A cewar Abdullahi, daga karɓar rahoton, sai hukumar ta yi maza ta tura jami’an ta na ɓangaren bada agaji, inda su ka isa wajen da misalin ƙarfe 5:04 na yamma.

Da zuwan su, in ji Abdullahi, sai su ka ɗauko Hamida, amma tuni rai ya yi halin sa, inda su ka miƙa gawar ta ta zuwa ga yayanta, Abdullahi Bawale.

Kakakin ya ƙara da cewa marigayiyar ta gamu da ajalin ta ne bayan da ta je debo ruwa a rijiyar shi ne ta faɗa ciki.

Sai dai kuma sanarwar ta ce Hamida na fama da ɗan taɓin hankali.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet