Labarai
Ƴan sanda a Kano sun cafke wasu ɓarayin dabbobi da dillalinsu

Jami’an ƴan sanda a jihar Kano sun samu nasarar cafke wasu ɓarayin dabbobi da suka addabi ƙauyen Aujawarar Alkali da ke yankin Ƙaramar Hukumar Gezawa.
Haka kuma jami’an tsaron sun cafke wanda ya ke sayen dabbobin satar daga hannun baraynin.
Kakakin ƴan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafko ‘barawon zaunen’ ne a yayin da ake gudanar da bincike bayan an kama barayin tumakin.