Featured
Dakatar Da Sheikh Nuru Khalid: Abubuwan Da Ya Kamata Mutane Su Sani

Ina so na yi ƙarin haske kan wasu abubuwa a taƙaice, waɗanda dayawan mutane ba su sani ba game da batun dakatar da Sheikh Khalid.
1- Da farko ya kamata a sani cewa masallacin da Sheikh Nuru Khalid yake aiki a matsayin babban limanci wato “Apo Legislative Quarters Juma’at Mosque” masallaci ne na gwamnati, ba na wani mutum bane ko wasu jama’a ko ƙungiya. Kai da jin sunan unguwar ” Legislative Quarters” wato unguwar ƴan majalisar dokoki, kasan harkar gwammati ce.
2- Limancin da Sheikh Khalid yake a masallacin leburanci ne, kamar yadda gwamnati ko kamfani yake ɗaukar ma’aikata, haka aka ɗauki Sheikh Nuru Khalid aikin yin limanci a wannan masallaci. Albashi ake biyan sa mai tsoka, haɗi da tagomashi da yake samu daga jami’an gwamnati.
3- Masallacin yana da tsare-tsare dokoki waɗanda duk wanda aka ɗauka aikin yin limanci to fa dole sai ya bi su, kamar yadda dai ka sani ma’aikata ko kamfani suna da tsare-tsare da dokoki waɗanda kowane mutum da aka ɗauka aiki sai ya bi su haka shima masallacin yake.
4- Daga cikin waɗannan dokokin, liman bai isa ya faɗi wani abu a cikin huɗuba ba, ba tare da sahhalewar kwamitin masallaci ba, dole sai kwamitin masallaci ya tantance, kwamiti ne suke tsara wa liman irin maudu’in abin da ake so ya riƙa yin huɗuba a kai, sa’an nan, idan ya rubuta huɗuba to dole sai ya kawo ta gaban kwamitin, sun tantance ta kafin a ba shi damar ƙaddamarwa, idan aka ga wasu abubuwa cikin huɗubar waɗanda ba a so, za a umarce da ya cire su, kuma dole ne ya yi a matsayinsa na lebura.
5- Ga wanda ya karanta takardar dakatar da Sheikh Khalid wadda kwamitin ya fitar, zai ga cewa, sun tuhume shi ne da karya dokar aiki, yana yin kalamai waɗanda kwamiti bai lamunce masa ba, kuma an sha ja masa kunne amma ya ƙi bari.
6- Wannan shi ne haƙiƙianin yanayin masallacin da kuma yanayin tsarin aiki a cikinsa, masallacin Central Mosque wanda Pro. Ibrahim Maqari yake limanci da kuma masallacin Wuse Zone 2 wanda malam Isa Pantami yake limanci, suma duka tsari ɗaya ne. Kuma suma da a ce suma za su faɗi irin abin da ya faɗa, da sai an ci musu mutunci sama da yadda kake tunani. Tunda idan malam Nuru Khalid mai interfaith, irin aƙidar da ake so a hukumance, za a takarar da shi don ya saɓa doka, to ina kuma ga waɗanda addini musulunci suke karantarwa da karewa?
7- Na goyi bayan kalaman Sheikh Khalid saboda gaskiya ya faɗa, amma kuma shi kansa ya san wannan wajen ba wajen faɗin gaskiya ba ne, da a ce ya ajiye aikin, sa’an nan sai ya yi amfani da shafinsa na soshiyar mediya ko kuma wani wajen ya yi caccakar gwamnati yadda ya so, da ba mu ji labarin dakatar da shi ba. Dama fa shi malamin da yake aiki ƙarƙashin gwamnati dole ba kowace gaskiya zai iya faɗa ba, in dai yana son aikinsa.
8- A dokar ƙasan nan suna da sashen ƴancin faɗin albarkacin baki, da bayyana ra’ayi, kowane irin ra’ayi ne kuwa, shi ya sa za mu ga Bishop Matthew Kukah ya faɗi wadda ta fi ta Sheikh Khalid za fi, don shi za a iya fassara wasu kalaman na sa da cin amanar ƙasa, haka nan wani Pastor Suleiman Johnson har umarni ya ba wa membobin cocinsa kan su kashe Fulani idan suka gan su kusa da cocin. Haka nan ko Lahadin nan ɗaya daga cikin manyan fastocin ƙasar nan wato Pastor E A Adebayo ya caccaki gwammati kan harin Kaduna, kuma babu abin da ya faru da su, babu wanda ya dakatar da su. Shi ma Malam Bello Yabo yana yin caccaka kuma babu mai dakatar da shi, tunda babu wanda ya sa shi, babu wanda yake biyansa.
9- Su waɗannan shugabannin babu Allah a ransu fa, duniyarsu kawai ce ta dame su, watarana wannan kama-karyar za ta zo ƙarshe, laifin Sheikh Khalid shi ne maƙalewa da ya yi tare da su, tunda ya gane gaskiya, sai fita daga cikin marasa gaskiya.
Allah Ya datar da mu.
Isa Sadi ya rubuto daga Kano – Najeriya.