Connect with us

Labarai

Shagulgulan Sallah: Murtala Garo ya buƙaci mutanen Kano su ci gaba da haƙuri da haɗin kai don wanzuwar zaman lafiya

Tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar Kano kuma mai neman takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Sule Garo, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi koyi da darussan da suka koya a watan Ramadana mai albarka tare da inganta ɗabi’ar haɗin kai da zaman lafiya domin ci gaban jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

Alhaji Murtala Sule Garo, ya buƙaci hakan ne ta cikin saƙonsa na Barka da Sallah ga al’ummar Musulmi wanda ya aike wa da shafin jaridar Internet na Kakakihausa.

Ta cikin sanarwar kwamishinan ƙananan hukumomin na Kano mai murabus ya jaddada buƙatar da ke akwai ta samun haɗin kai da haƙuri domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Haka kuma, ya buƙaci Musulmin jihar Kano da su yi amfani da lokacin bukukuwan Sallar wajen yin tunanin ayyukan da suka yi a baya domin gyara kurakuran da suka aikata.

Ya kuma ce, “Akwai buƙatar al’umma su yi koyi da Manzon Allah SAW wajen sadaukarwa a harkokinsu na duniya, domin amfanar da marasa galihu a cikin al’umma.”

Galadiman na Garo ya bukaci mutane a lokacin bikin da cewa kada su manta da halin karamci da kuma tallafa wa marasa ƙarfin da suke tare da su.

“Ina amfani da wannan dama domin taya gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje murnar kammala azumin watan Ramadana lafiya da kuma shaida bikin Sallah,” in ji sakon.

“Haka kuma, ina taya Sarakunanmu na masarautu 5 murna da kuma al’ummar Kano tare da goyon bayan gwamnatin Gwamna Ganduje bisa yunƙurin gina sabuwar Kano domin amfanin al’umma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet