Labarai
Majalisar dokokin Kano ta ɗage komawa aiki daga hutun Azumi

Majalisar dokokin jihar Kano, ta sanar ɗage komawa domin ci gaba da gudanar da zamanta daga yau Litinin 16 ga watan Mayu har sai ranar Litinin 6 ga watan Yuni.
Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari wakilin ƙaramar hukumar Makoda a majalisar shi ne ya bada umarnin ɗage komawar.
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na majalisar Uba Abdullahi, ya fitar da yammacin yau Lahadi.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, majalisar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a sabuwar ranar da ta sanya da zarar ta koma bakin aiki.