Labarai
Kano: Adadin mutanen da suka mutu a fashewar gas ya ƙaru zuwa 9

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mutanen da suka mutu sakamakon fashewar iskar gas a Kano ƙaru zuwa mutane 9.
Hukumar bada agajin gaggawa ta tarayya NEMA ce ta bayyana hakan lokacin da babban daraktan hukumar Malam Mustapha Habib Ahmed, ya ziyarci wurin da iftila’in ya faru.
Bayan faruwar lamarin dai Ko da yake a baya kwamishinan ƴan sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya tabbatar da mutuwar mutane 4, kafin daga bisani adadin ya ƙaru.
Hukumar ta NEMA, ta ce, an gano gawarwaki 9 daga ɓaraguzan ginin.
da ya ruguje a gefen wata makarantar firamare sakamakon fashewar wani bututun iskar gas a hanyar Aba dake unguwar Sabon Gari a jihar Kano.