Labarai
Kotu ta dakatar da shugabanncin PDP ɓangaren Shehu Wada Sagagi a Kano

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Kano ta dakatar da shugabancin jam’iyar PDP, ƙarƙashin Shehu Sagagi har sai ta gama sauraron ƙarar da a ka shigar a gaban ta.
Ana zargin Sagagi da biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso.
Wani Bello Bichi ne ya shigar da ƙarar a gaban Mai Shari’a A. M. Bichi, inda ya yi ƙarar jami’yyar PDP da hukumar INEC da kuma sauran mutane 40.
Kotun ta ce ta bada umarnin ne domin gujewa wani yanayi da za a zama babu shugabci a jam’iyar, shi ya sanya ta bada umarnin ga wanda a ke ƙara na 3 har zuwa na 42.