Siyasa
Sanata Shekarau ya karɓi katin jam’iyyar NNPP

Tsohon gwamnan Kano, kuma ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya karɓi katin zama mamba a jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.
Dubban magoya bayan Sanatan da kuma na jam’iyyar ta NNPP ne suka shaida karɓar katin Jami’yyar a gidansa da ke kan titin Mundubawa a Kano.
Yayin karɓar katin nasa dai, Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya halarci gangamin taron sauya sheka a hukumance ya mikawa Sanata Shekarau katin zama dan jam’iyyar NNPP.