Labarai
INEC- Ba za mu sake ajiye kayan zaɓe a banki ba

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce, ba za ta sake kai wa babban bankin Najeriya CBN ajiyar kayan zaɓe masu muhimmanci ba.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne, ya bayyana hakan.
Farfesa Mahmood ya bayyana hakan ne ta cikin jawabinsa a wani taron ƙara wa juna sani a ƙarshen makonnan a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, hukumar za ta fara daina ajiye muhimman kayan ne daga zaɓen baɗi da ke ƙaratowa.