Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, ne ya jagoranci gwamnonin wajen halartar taron a yau Talata.
Jaridar Internet ta Solacebase ta ruwaito cewa, Duk da gwamnonin ba su yiwa manema labarai bayanin dangane da maƙasudin taron ba, amma Rahotonni sun bayyana cewa, an gudanar da taron ne kan wanda zai zama mataimaki ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Haka kuma rahotonni sun cewa, manyan muƙarra gwamnatin tarayya da suka halarci taron sun haɗa da: Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapaha da sauransu.
Sai gwamnoni da suka haɗa da: Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da Nasiru el-Rufa’i na Kaduna, da gwamnan Jigawa Muhammad Badaru, da gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, da Simon Lalong, na Filato da Yahaya Bello, na Kogi da Dave Umahi na jihar Ebonyi da kuma gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma.
