Wasanni
Ƴar wasa Tobi Amusan ta samu nasara a gudun mita 100

Yar wasan Najeriya, Tobi Amusan ta kafa sabon tarihi bayan da ta lashe kyautar zinare a gudun mita 100 na gasar Commonwealth da aka yi a birnin Birmingham na kasar Birtaniya.
Mai shekaru 25, Yar wasan ta kafa sabon tarihin be, makwanni biyu bayan da ta zama ‘yar wasan Najeriya ta farko da ta lashe zinare a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya yayin da ta kai ga samun nasara a gasar tseren mita 100 na mata a Oregon.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, ta shafe tarihin duniya a wasan kusa da na ƙarshe a filin wasa na Hayward a cikin dakika 12 da sakan 6.