Wasanni
Majalisar dokoki za ta yi bincike kan matsalolin da suka addabi Kano Pillars

Majalisar dokokin jihar Kano, za ta gudanar da bincike kan tarin matsalolin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ke fama da su.
Hakan na Rahotonni sun bayyana cewa, a zamanta na Litinin ɗin makon nan, umarci kwamitin ta mai kula da harkokin wasanni kan ya gudanar bincike kan musababbin matsalolin ƙungiyar.
Majalisar ta umarci Kwamitin ne bayan amincewa da kudirin gaggawa wanda ɗan majalisa mai wakiltar Rano Alhaji Nurudeen Alhassan kuma shugaban kwamitin kula da wasanni ya gabatar.
Haka kuma ya bayyana wasanni a matsayin ginshiƙin ci gaban harkokin matasa.
Mamban na Rano, ya kuma shaida cewa ƙungiyar ta Kano Pillars a yanzu haka ta faɗa cikin mawuyacin hali don haka yake so majalisar ta kai mata ɗaukin gaggawa.