Featured
Farfesa Gwarzo ya baiwa daliba mafi kwazo a Jami’ar Yusuf Maitama Sule kyautar Naira Miliyan Ɗaya ₦1m

Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bada gudummawar naira Miliyan Ɗaya ga wata ɗaliba da ta kammala karatu a makarantar North West University Kano, wadda yanzu ake kira da Yusuf Maitama Sule University.
Maimuna Umar Zarewa, ta kammala karatun digirinta na farko a Bsc Chemistry a tsohuwar Jami’ar Arewa maso Yamma ta Kano a shekarar 2017, ta kuma samu irin wannan nasarar a matsayinta na babbar dalibar da aka yaye a Sashin Chemistry na Jami’ar Bayero Kano, baya ga samun gurbin karatu na kasa-da-kasa kan digirinta na uku, a kasar Saudi Arabia.
Da yake sanar da bayar da tallafin, Farfesa Adamu Gwarzo ya yaba wa Zarewa bisa nasarorin da ta samu tare da jaddada mahimmancin saka hannun jari ga matasa masu fasaha irin su.
Ya kuma bai wa ɗalibar takardar shaidar kwazo domin zaburar da sauran dalibai wajen fuskantar karatunsu da dukkan abin da ya dace.
Farfesa Gwarzo ya bayyana Zarewa a matsayin daliba mai hazaka, ƙwazo da kuma zalaka, wanda burinta na samun ƙwararren ilimi, idan aka tallafa mata zai ba ta damar cimma burinta a rayuwa.
Ya kuma bayyana cewa ilimi ya kasance ginshikin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kowace kasa, yana mai nuni da cewa idan Najeriya za ta ba da fifiko a fannin, kasar za ta zama daya daga cikin kasashen da suka ci gaba.
Da take mayar da martani, Maimuna Umar Zarewa ta godewa Farfesa Gwarzo bisa wannan karamcin inda ta kara da cewa babu wanda ya bayar da gudunmuwarta wajen neman ilimi, banda iyayenta kamar Farfesa Gwarzo.
Ta kuma bayyana cewa, Farfesan shi ne da hannu wajen shigarta Jami’ar Tarayya ta Dutsinma a matsayin Malama, kuma a lokaci guda ya taimaka mata wajen samun gurbin karatu na digiri na uku a kasar Saudiyya.
Bilkisu Zarewa ta godewa wadanda suka shirya shirin tare da shawartar sauran daliban Jami’ar da su fuskanci karatunsu da gaske domin samun nasara a rayuwa.