Labarai
Buhari Zai Kai Ziyara Maiduguri Ranar Alhamis

An kammala duk wani shirin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara Maiduguri ranar Alhamis.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa ziyarar ita ce ziyarar aiki ta uku da shugaban ya kai Maiduguri cikin shekara guda bayan ta 17 ga watan Yuni da 23 ga watan Disamba a shekarar 2021.
A lokacin da yake Maiduguri, ana sa ran Buhari zai kaddamar da tallafin jin kai ga marasa galihu, da gudunmar kwararrun malamai a Bukumkutu da kuma gidaje 500 a Molai da gwamnatin jihar ta samar.
Ana kuma sa ran zai yi mubaya’a ga Shehun Borno.
An shawarci jama’a da ke kan hanyar wucewa da su tashi da wuri domin gujewa toshe hanyoyin da irin wadannan ziyarce-ziyarcen ke haifarwa.